in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban hukumar aikin kiyaye zaman lafiya ta MDD ya kai ziyara cibiyoyin MDD a yammacin Sahara
2012-10-11 10:19:32 cri

Mai magana da yawun MDD, Martin Nesirky ya bayyanawa manema labaru cewar, karamin magatakarda na harkokin kiyaye zaman lafiya ta MDD, Herve Ladsous, ya isa garin Laayoune ran Laraba, don ziyartar cibiyoyin MDD dake yankin, dangane da batun kuri'a da za'a yi a yankin yammacin Sahara wanda a kaiwa lakabi da MINURSO.

Yayin jawabin da aka saba yi yau da kullum ga 'yan jarida, Nesirky ya kara da cewa, Ladsous zai gana ne da shugabannin cibiyoyin na MDD, sannan zai yi nazarin yadda suke tafi da ayyuka, kana zai kai ziyara wurare biyu, zai kuma je yankunan Tindouf da Rabat, inda zai gana da jami'an bangarorin biyu.

Ladsous har wa yau, zai tattauna da bangarorin biyu dangane da takaddama tsakaninsu game da yankin.

Wannan ziyara ta Ladsous, ita ce ta farko da hukumar aikin kiyaye zaman lafiya ta MDD ta yi zuwa MINURSO a cikin shekaru 14.

Hukumar ta MDD da aka kafa a shekarar 1991 tana dauke da nauyin sa ido kan batun tsagaita wuta a yankin yammacin Sahara, da kuma gudanar da kuri'a kan batun samun 'yancin kai ga mutanen yankin.

Tun shekarar 1976 ne MDD ke kokarin yin daidaito a yankin yammacin Sahara, sakamakon barkewar fada tsakanin Morocco da kuma kungiyar Polisario bayan karewar mulkin mallakar da Spaniya ta yi a yankin.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China