Bisa kididdigar tattalin arziki ta watan Maris da kasashen Afirka dake kudu da hamadan Sahara suka bayar, an ce, kasashen Afirka ta kudu, Nijeriya, Kenya, Uganda, da kuma Tanzania suna fuskantar hauhawar farashin kaya. Yawan hauhawar farashin kaya na kasar Kenya ya karu watanni 5 da suka gabata, yawansa na watan Maris ya kai kashi 9.19 cikin kashi dari, a ciki, farashin gidaje, ruwan sha, wutar lantarki, abinci da kuma makamashi sun fi samun karuwa.
Manazarta sun bayyana cewa, yanayin hauhawar farashin kaya zai kawo illa ga zaman rayuwar jama'a da kamfanoni kanana da matsakaita a kasashe da dama dake kudu da hamadan Sahara, kana zai kawo cikas ga samun bunkasuwar tattalin arzikinsu a wannan shekarar, da kuma haddasa rikice-rikice a fannin siyasa. Yanzu dai, wasu kasashe sun riga sun dauki matakai don tinkarar hauhawar farashin kaya.(Zainab)