in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon MDD ya bukaci bangarorin da abin ya shafa game da yankin yammacin Sahara da su koma kan teburin sulhu
2012-11-13 10:22:37 cri

Wakilin babban sakataren MDD game da yankin yammacin Sahara Christopher Ross, ya yi kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa da su shiga abin da ya kira, "tattaunawa ta zahiri da sulhuntawa don lalubo bakin zauren warware batun matsayin yankin yammacin Sahara kwata-kwata."

Mr. Ross wanda ke ziyara a arewacin Afirka da nahiyar Turai daga ranar 27 ga watan Oktoba zuwa 15 ga watan Nuwamba, ya bayyana hakan ne a Madrid ranar Litinin ga manema labarai, bayan ya gana da ministan harkokin wajen kasar Spain, Jose manuel Garcia-Margallo.

Kakakin MDD Martin Nesirky ya bayyana cewa, wakilin babban sakataren MDD ya fada cikin wata sanarwa cewa, an dade ana kai ruwa rana game da matsayin yankin yammacin Sahara, don ya ce, yana ganin matsalar za ta ci gaba ganin yadda ake samun barazanar karuwar masu tsattsauran ra'ayi, 'yan ta'adda da kuma munanan ayyuka a yankin Sahel.

Ross ya ce, za a warware wannan matsala ce kawai muddin aka koma ga tattaunawa ta hakika da sasantawa, ta yadda za a kawo ga karshen matsalar baki daya. Don haka, ya bukaci bangarorin da abin ya shafa, da su koma ga teburin sulhu, sannan ya bukaci al'ummomin kasa da kasa, da su yi amfani da kwarewarsu don ganin sun karfafawa bangarorin gwiwar yin hakan.

Nesirky ya ce, bayan ziyarar da Ross zai kai Madrid, har ila ana sa ran zai ziyarci birnin Paris a ranar Talata, sannan zai zarce zuwa Washington, London da kuma Moscow nan ba da dadewa ba , don tattaunawa da su.

A ranar 7 ga watan Janairun shekara ta 2009 ne aka nada Ross, tsohon jakadan kasar Amurka a kasashen Algeria da Syria a matsayin manzon babban sakataren MDD mai kula da batun yammacin Sahara.

Kafin nadin nasa, shi ne mai bai wa tawagar Amurka shawara ta musamman a MDD game da yankin gabas ta tsakiya da arewacin Afirka.

Tun a shekara ta 1976 ne MDD ke kokarin daidaita batun yammacin Sahara, tun lokacin da fada ya barke tsakanin Morocco da yankin Polisario bayan karewar mulkin mallakar kasar Spaniya a yankin, inda Morocco ta ayyana 'yancin yankin, amma sai yankin na Polisario ya yi imanin cewa, kamata ya yi a yanke shawarar kasancewar matsayin yankin ta hanyar jefa kuri'ar jin ra'ayin jama'a. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China