in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon MDD ya fara ziyarar aiki a yankin yammacin Sahara
2013-03-21 10:57:53 cri

Manzon musamman ga babban sakataren MDD mai lura da sashen yammacin Sahara Christopher Ross, ya isa birnin Rabat na kasar Morocco a ranar Laraba 20 ga watan nan, domin fara wata ziyarar aiki a yankin yammacin Sahara.

Yayin ganawarsa da manema labaru, kakakin MDD Martin Nesirky, ya ce, Ross zai kammala ziyarar tasa ne ranar 3 ga watan Afrilu mai zuwa. Yayin wannan ziyara, ana sa ran Ross zai gana da manyan jami'an hukuma, da 'yan majalissun dokoki a birnin na Rabat. Rabat shi ne birnin na farko da jakadan zai yada zango, yayin wannan ziyarar da ya fara a arewacin nahiyar ta Afirka, kafin ragowar yankunan yammacin Sahara, inda zai tattauna da hukumomin kasashen Algeria da Mauritania.

Makasudin ziyarar tasa dai shi ne share fagen tattaunawa a mataki na gaba, domin cimma daidaito kan turbar siyasa, da ba da damar rungumar shawarwari a siyasance, wadanda za su kawo karshen sabanin dake tsakanin Morocco da yankin nan na Frente Polisario.

Rikici ya barke tsakanin Morocco da wannan yanki ne, biyowa bayan kammalar mulkin mallaka da kasar Sifaniya ta yi wa yankin cikin shekarar 1976, inda daga bisani MDD ta sanya baki a yunkurinta na shiga tsakani. A baya dai, Morocco ta ambata baiwa yankin na Frente Polisario damar cin gashin kai, sai dai yankin ya zabi a gudanar da kuri'ar raba gardama, wadda za ta kunshi batun samun ikon ballewa, da samun yancin kai, a matsayin hanyar kawo karshen wannan takaddama.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China