A kwanan nan, wani shahararren kamfanin kula da ayyukan zuba jari na kasar Amurka ya bayar da rahoto cewa, ko da yake kasancewar dimbin matasa a kasashen Afirka da ke Hamadar Sahara ta kudu wani kalubale ne gare su,duk da haka suna iya jawo jarin da ke bukatar dimbin mutane, ta yadda za a sa kaimi ga ci gaban tattalin arzikin wurin. Haka zalika kuma, yaduwar fasahar ban ruwa za ta inganta bunkasuwar tattalin arziki sakamakon kasancewar yawancin manoma na fama da karancin ruwa a gonarsu.Gwamnatin kasar Kenya tana kokarin yiwa tsarin ban ruwa kwaskwarima, kuma ta kebe kudi Dala miliyan 22 domin gina madatsar ruwa, duk a kokarin samun ci gaba.
Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, a cikin shekaru 10 da suka gabata, matsakaiciyar jimillar GDP da kasashen Afirka 49 da ke Hamadar Sahara ta kudu sukan samu na karuwa da kashi 5.7 cikin kashi dari a ko wace shekara.(Kande)