Ya zuwa daren ran 31 ga watan Janairu da karfe 11 da minti 30 na agogon wurin, fashewar bom da aka yi a wannan rana da yamma a ginin kamfanin man fetur na kasar Mexico a birnin Mexico hedkwatar kasar ta yi sanadin mutuwar mutane 25 yayin da wasu 101 suka jikkata.
Ministan harkokin gida na kasar Osorio Chang ya gabatar da wannan adadi a wani taron manema labaru da aka yi a wannan rana da dare a wurin da bom din ya fashe.
Chang ya ce, ya zuwa yanzu, ma'aikata kimanin 500 ciki hadda 'yan sanda da sojoji suna aikin ceto. Kuma ana kokarin bincike kan lamarin, kuma za a gabatarwa kafofin yada labaru bayyanai da zarar an samu wani sakamako. (Amina)