Bisa rahoton da aka bayar, an ce, a wannan rana da misali karfe 9 da safe, wani mutum da ke dauke da bindiga ya shiga makarantar midil da ke birnin na Taft, sannan kuma ya bude wuta, lamarin da ya jikkata mutane 2.
Yayin da wannan lamari ke tada hankulan al'ummar kasar, shugaban kasar Barack Obama ya nada mataimakinsa Joe Biden don tsara matakan da za a dauka, wajen sa kulawa game da batun mallakar bindigogi a kasar. A ranar 10 ga wata, Biden ya yi shawarwari da mambobin kungiyar bindigogin kasar, wadda ke nuna goyon baya ga mallakar bindiga cikin 'yanci. Bayan shawarwarin, Biden ya jaddada cewa, ko da yake yanzu ba wata hanyar da za a bi wajen hana harbe-harben bindiga, amma lokaci ya yi da za a dauki wani mataki don magance irin wannan lamari. An bayyana cewa, kafin ranar 15 ga wata, Biden zai fitar da wasu matakai don kara sa kulawa game da mallakar bindigogi daga duk fannoni, kuma zai mika su ga shugaban kasar Amurka Barack Obama.(Bako)