Bisa labarin da 'yan sandan jihar suka bayar, an ce, wannan al'amari ya abku ne a makarantar firamare da ake kira Sandy Hook a safiyar ranar 14 ga wata, inda yara 18 suka mutu nan take yayin da wasu guda 2 suka mutu a asibiti bayan samun raunin mai tsanani da suka samu ban da haka, 'yan sanda sun samu gawawwakin matasa 6 a wurin, tare da gawar maharbin.
Dadin dadawa, a wani wuri na daban dake da alaka da wannan hadari, an tarar da gawar wani matshi na daban. A sabili da haka, yawan mutanen da suka mutu ya kai 28 a sakamakon, wanda ya kai matsayi na biyu bisa yawan mutane da aka kashe a makarantun Amurka cikin tarihi.Kafin faruwar haka an taba kashe mutane 33 a jami'ar Virginia ta Amurka, wanda ya kai matsayi na farko.
Kafofin yada labarai na wurin sun ba da labarin cewa, ana tuhumar Ryan Lanza, mai shekaru kimanin 20 da haihuwa, da aikata wannan laifi, yayin da 'yan sandan suka tsare dan uwansa domin yin bincike.
Game da wannan batu kuma, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi jawabinsa a fadar shugaban kasar a wannan rana, inda ya bukaci a dauki matakai domin dakatar da sake abkuwar irin wannan mummuman lamari.(Fatima)