Bangaren 'yan sanda na kasar Nijeriya ya ce, an samu wannan fashewar boma-bomai ne a kusa da wurin shirya aikace-aikace game da bikin murnar cika shekaru 50 da Nijeriya ta samu 'yanci daga Turawan mulkin mallaka na kasar Burtaniya. Amma, ba a dakatar da bikin ba sakamakon lamarin.
Bayan abkuwar lamarin, kungiyar neman hakkin yankin Niger Delta ta kasar Nijeriya, wato MEND ta yi shelar daukan alhakin lamarin, ta kuma bayyana cewa, sun yi haka ne don nuna adawa da bikin.
Yanzu, mutanen da suka ji rauni suna samun jinya a asibiti. Bangaren 'yan sanda kuma yana bincike kan lamarin. (Bilkisu)