Tun daga ranar 19 zuwa 22 ga watan Maris da ya gabata ne dai, wata tawagar CRI mai kunshe da mutane 4 sun ziyarci kasar ta Nijeriya, don zabar 'yan wasan kwaikwayo masu magana da Hausa, kuma bayan tantancewa har zagaye uku, 'yan wasan kwaikwayo guda shida, wadanda suka samu karbuwa a kasar ta Nijeriya, sun cimma nasarar zamowa zababbu da za su yi wannan aiki, sun kuma sanya hannu kan yarjejeniyar sanya murya a fassarar wannan wasan na Sinanci tare da bangaren tawagarta Sin. Cikin mutanen shida, tuni hudu suka iso nan birnin Beijing a yau.(Maryam)