Jagoran kwamitin lura da harkokin da suka jibanci albarkatun mai da iskar Gas a masarautar Nembe, Mr. Nengi James ne ya tabbatar da faruwar wannan lamari, yana mai cewa wasu al'ummomin yankin ne suka lura da kwararar da man yake yi a kan kogi, da sauran magudanan ruwan yankin.
Mr. James yace tuni suka sanarda kamfanin SPDC, wanda shine kamfanin dake aikin hakar man a wannan yanki, game da faruwar al'amarin, tare da kira ga al'umma da su ci gaba da juriya, yayin da ake kokarin shawo kan wannan lamari, musamman ma ganin yadda a cewarsa har izuwa yanzu, kamfanin na SPDC, ya gaza ziyarar yankin da wannan matsala ta auku. James ya kara da cewa, ya shaida aukuwar irin wannan matsala ta malalar mai har sau 10, tun kama aikin sa a matsayin Jagoran kwamitin lura da harkokin da suka jibanci albarkatun mai da iskar Gas a masarautar ta Nembe, sai dai abin takaici ne yadda kawo wannan lokaci, ba a gudanar da aikin kwashe koda daya, daga cikin man da ya zuwa zuba a sassan yankin ba.
Daga nan sai ya bayyana irin yadda a cewarsa, kamfanonin dake hakar mai ke rikon sakainar-kashi da wannan batu, matakin da ya ce sam, ba abu ne da za su amince da shi ba, musamman ganin yadda man, da kan malala ke gurbata ruwan dake kwance a sassan yankin. Bugu da kari james ya yi kira da mahukunta, da ragowar masu ruwa da tsaki, su dauki matakan shawo kan wannan matsala ba tare da bata lokaci ba. (Saminu Alhassan)