A cikin wadannan sabbin mambobi guda 25, jam'iyyar dake rike da ragamar mulkin kasar da kuma kungiyar siyasa dake adawa kowannensu na da mambobi guda 10, sannan 'yan tsaka tsaki da kuma wakilan jama'a na da mambobi guda 5.
Sabon shugaban da aka zaba Bakary Fofana shi ne wakilin jama'a, sannan wakilai guda biyu suna kan matsayin mataimakin shugaba, inda mataimakin shugbanni biyu suna wakiltar jam'iyya mai rike da ragamar mulkin kasar ne na yanzu, saura biyu kuma wakilai ne daga kungiyar adawa. Bisa labarin da aka samu, an ce, hukumar zaben mai zaman kanta za ta gabatar da wani jadawali na gudanar da zaben majalisar dokoki ga gwamnatin kasar a cikin 'yan kwanaki masu zuwa, kana za ta yi aikin share fage domin zaben.
A cikin watan Satumba na bana, kungiyar adawa ta nuna rashin amincewarta kan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Guinea, inda hakan ya sa shugaba na lokacin ya yi murabus tare kuma da tsai da shawarar yin gyare-gyare na jerin jami'an hukumar zaben.
Bayan babban zaben kasar na Guinea da aka yi a shekarar 2010, jam'iyya dake rike da ragamar mulki da kuma kungiyar da ke adawa ba su cimma ra'ayi daya ba, kan wasu batutuwan da suka shafi zaben, inda wannan lamari ya sa an yi ta jinkirin zaben majalisar dokoki.
Kan wannan, shugaban kasar Alpha Conde ya nuna cewa, zai dukufa matuka domin gudanar da zaben majalisar dokoki cikin adalci a fili ta hanyar dimokuradiya a karshen shekarar 2012 ko kuma a farkon shekarar 2013. (Maryam)