in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Guinea ta yi kira ga jam'iyyun adawa da su taimakawa gudanar da zaben majalisar dokokin kasar
2012-10-20 17:40:06 cri
A ranar Jumma'a 19 ga wata, gwamnatin Guinea ta fidda sanarwar yin Allah wadai da jam'iyyun adawa da su jinkirta yunkurin shiga zaben majalisar dokokin kasar, kuma ta yi kira ga shugabannin jam'iyyun adawa da su sauke nauyin dake bisa wuyansu wajen kammala aikin share fagen shiga zaben cikin sauri, a kokarin taimakawa gwamnatin kasar wajen gudanar da wannan zaben yadda ya kamata.

Sanarwar ta ce, tun bayan da aka yi kwaskwarima ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Guinea a watan Satumba na bana dake da nauyin shirya zaben majalisar dokokin, jam'iyyun adawa ba su gabatar da sunayen 'yan takararsu bisa lokacin da aka kayyade ba. Idan hukumar zaben ba za ta kammala aikin gyare-gyare a watan Oktoba na bana ba, wannan zai yi tasiri ga gudanar da zaben kai tsaye.

Dadin dadawa, sanarwar ta jaddada cewa, idan jam'iyyun adawa su ki gabatar da sunayen wakilansu, gwamnatin kasar za ta nemi hanyar daidaita batun bisa dokoki, a kokarin sa kaimi ga gudanar da zaben, ta yadda za a kammala yanayin wucin gadi na mulkin kasar Guinea tun da wuri.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China