in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Alpha Conde na barazanar daukar matakan ladabtarwa kan mutanen da ake zargi da sama da fadi da dukiyar kasa a Guinea
2012-06-04 15:26:50 cri
Shugaban kasar Guinea Alpha Conde ya sanar da daukar matakan gaggawa a cikin yakin da yake da cin hanci da rashawa ta hanyar shirin gurfanar duk wasu mutanen da ake zargi da yin sama da fadi da dukiyar kasa. Shugaban kasar ya yi wannan furuci ne a yayin wani taron gangami na kwawancen matasan kasar a Conakry a ranar Asabar, a wani labarin da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu daga wata majiya mai tushe.

Cikin wani yanayi na bacin rai ne, shugaba Alpha Conde na nuna korafinsa kan mutanen da a cewarsa suke maida kasa baya.

Tare kuma da yin Allah wadai da mutanen da suke amfani da matasa wajen gurfanar da wannan kasa, ana maida ta baya ga tsara a yammacin Afrika maimakon su daga tutar kasar zuwa matsayin farko, ganin yadda kasar Allah ya hore mata da dimbin albarkatu.

Alpha Conde ya bayyana ba tare da rufa rufa ba, cewa "kasar Guinea ta sa kai gaba" a halin yanzu a gaban idon wadanda suka gurfanar da kasar, ya nuna cewa, abun da ba'a yi ba a cikin shekaru 25 ana kokarin yin shi a cikin shekaru biyu kawai. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China