Ranar 21 ga wata, a lokacin da suke zanga-zanga, wasu matasan da ke goyon bayan 'yan adawa sun ta da rikici tare da wadanda suke goyon bayan jam'iyyar da ke mulkin kasar, lamarin da ya haifar da tarzoma. A daren wannan rana, kuma jami'an tsaron kasar sun bayyana cewa, wani ya mutu sakamakon tarzomar, yayin da wasu 46 suka jikkata, ciki har da 'yan sanda 13. A ranar 22 ga wata, wasu magoya bayan 'yan adawa sun ci gaba da yin zanga-zanga a wasu sassan birnin Conakry, wadanda suka kone tayoyi domin toshe muhimman hanyoyi, daga baya 'yan sanda sun tarwatsa su. Yanzu dai kura ta kwanta a Conakry. A daren ranar 21 ga wata, shugaba Alpha Conde na Guinee ya yi kira ga jama'ar kasar da su yi hakuri, a kokarin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar. (Tasallah)