in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kwamitin zabe mai zaman kansa na kasar Guinea ya yi murabus
2012-09-06 14:57:47 cri
A ranar 5 ga wata da dare ta gidan rediyon kasar Guinea, shugaban kwamitin zabe mai zaman kansa Louceny Camara ya sanar da yin murabus daga mukaminsa, kuma yana fatan ta wannan hanya za a sassauta takadama dake tsakanin jam'iyyar dake mulki da jam'iyyar adawa da kuma kara azama ga gudanar da zaben majalisar dokoki tun da wuri.

Bayan shugaban kasar Alpha Conde ya gana da shi a wannan rana, Louceny Camara ya sanar da yin murabus. A sa'i daya kuma, Louceny Camara ya kira jam'iyyun siyasa daban daban a kasar da su maida moriyar al'umma da kasar a gaban kome, tare da kawar da bambancin ra'ayi da kuma gudanar da zaben majalisar dokokin tun da wuri.

An ba da labari cewa, tun lokacin da kasar ta gudanar da babban zabe a shekarar 2010, jam'iyyar dake mulki da jam'iyyar adawa sun kasa cimma matsaya guda kan matsalar zaben majalisar dokokin kasar, lamarin da ya sa an jinkitar da lokacin yin zaben sau da dama. Jam'iyyar adawa ta bukaci Louceny Camara da ya yi murabus da kuma kafa sabuwar hukumar zabe. Kwanan baya, hukumomin kasar sun tarwatsa zanga-zangar da kungiyoyi masu yin adawa suka yi, daga baya, ministocin 'yan adawa guda biyu dake cikin gwamnati da mambobin dake cikin hukumar zabe guda 7 sun sanar da yin murabus domin kara matsin lamba ga hukumomin kasar.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China