in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin tekun kasar Sin za su gusa daga jerin tsibirai na farko don  horas da rundunonin jiragen ruwan sojan kasar
2013-01-30 17:00:01 cri
Bisa labarin da aka samu daga hukumar kula da harkokin watsa labarai ta ma'aikatar harkokin tsaron kasar Sin ran 30 ga wata, an ce, a 'yan kwanaki masu zuwa, sojojin tekun kasar za su gusa daga jerin tsibirai na farko don horas da rundunonin jiragen ruwan sojan kasar.

Jerin tsibirai na farko dai da Amurka ta kirkiro ya taso ne daga jerin tsibirai na Japan har zuwa na kasar Philippines, wadanda suka fi kusa da babban yankin kasar Sin.

An gudanar da wannan aiki ne bisa shirin horas da sojojin tekun kasar na shekarar 2013.

A bara, gaba daya sojojin tekun kasar Sin sun yi irin wannan horo sau bakwai.(Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China