in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Najeriya za ta hada gwiwa da wasu kasashe 10 domin gwagwarmaya da fashi a kan teku
2012-02-28 14:27:34 cri
Nijeriya da wasu kasashe guda 10 da su ka hada da Amurka, Belgium da Spain, sun soma atisayen bada horo ta ruwa a ranar Litinin 27 ga wata, wannan kuma domin gwagwarmaya da 'yan fashi kan teku da satar man petur, da fasa kwauri, da sauran matsaloli na tsaron teku da ake fuskanta a ruwan kasashen Afrika ta tsakiya da ta yamma, musamman a yankin mashigin tekun Guinee.

Sauran sojin ruwa da ke halartar atisayen sun fito daga kasar Kamaru, Gabon, Ghana, Congo Brazzaville, Benin, Sao Tome and Principe da Togo.

Babban hafsan –hafsoshin dakarun ruwa na Najeriya, Ola Ibrahim shi ne ya sanar da wannan labari ga 'yan jarida a ranar Litinin a garin Calabar, jihar Cross River da ke Najeriya. Wannan tsarin da ke gudana a Najeriya a garin Calabar an yi mashi suna da "Obangame Express 2012".

sojojin yakin ruwa na kasashe 11 ne ke halartar wannan atisaye da zai dauki tsawon sati guda .

A cewar Ola Ibrahim, wannan atisaye zai sa hulda sosai tsakanin sojojin ruwan kasashen da su ke halartar samun horon, kamar yadda ake so. Zai kuma tabbatar da cewa, sojojin yakin ruwan Najeriya da jiragensu na shirye don kai farmaki kamar yadda aikinsu ya tanada.(Abdou Halilou).

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China