Shugaban majalisar David Mark wanda ya bayyana haka a wani taro da rundunar sojin ruwan ta shirya a Abuja, fadar gwamnatin kasar don murnar cika shekaru 56 da kafuwa, ya ce yanzu haka ana yin duk abin da ya kamata don cimma wannan burin. Yana mai bayanin cewa, dogaron da kasar ke da shi akan jigilar jiragen ruwa don kara samun tattalin arzikin kasa da cigaba ya wajabta bukatar dake akwai na tabbatar da ganin an bata rundunar tsaro yadda ya kamata.
Ya ce, "Nigeriya na bukatar nagartaccen sojin ruwa don kaiwa matsayin ingantaccen sojin ruwa na kasar, da kuma hanyar tattalin arziki mai dorewa. Ya kara da cewa, karuwan fasa kwarin teku, lalata bututun mai, satar man krud, da safaran man fetur ta barauniyar hanya da kuma ta'addanci ya kara dora wani nauyi kan sojin ruwan kasan na ganin an kara samar da cikakken tsaro a sha'anin jigilar jiragen ruwan ta.
A cewar shugaban majalisar dattawan Nigeriyan, wani abun damuwa shi ne ganin kaddarorin kasar na miliyoyin dala na hako mai da ke cikin teku kamar na Bonga da Agbami suna fuskantar rashin tsaro yadda ya kamata saboda karancin kayan tsaro da rundunar sojin ruwan kasar ke da shi.
Shugaban majalisar dattawan David Mark, ya ce Nigeriya za ta yi sakaci ta fannin tsaro da tattalin arziki idan ta yi ma rundunar sojin ruwan ta rikon sakainar kashi. (Fatimah)