in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin ruwa na Sin da Rasha sun yi rawar daji tare a kasar Sin
2012-04-22 14:08:36 cri

A ranar Lahadi 22 ga wannan wata, sojojin ruwa na kasashen Sin da Rasha sun kaddamar da wata rawar daji mai suna "Hada Kai a Teku na shekarar 2012" a yankin tekun dake kusa da birnin Qingdao na kasar Sin. Wannan ne karo na farko da sojojin ruwa na kasashen biyu suka yi rawar daji cikin hadin gwiwa, kuma za a kawo karshen wannan rawar daji a ranar 27 ga wannan wata. Haka kuma, laftana-janar Ding Yiping, mataimakin babban kwamandan runduanr sojan ruwa ta kasar Sin ya bayyana cewa, an shirya wannan rawar daji ne ba domin wani bangare na daban ba.

Da misalin karfe 8 da minti 12 na yau da safe, manjon janar Leonid Sukhanov, mataimakin babban hafsan hafsoshin runduanr sojan ruwa na kasar Rasha shi ne ya yi shelar kaddamar da wannan rawar daji, sannan laftana-janar Ding Yiping ya sanar da shirye-shiryen wannan rawar daji da za a yi.

Babban taken wannan rawar daji shi ne "Yin aikin tsaron kai cikin hadin gwiwa da kuma taimakawa juna wajen jigilar kayayyaki da yin yaki". A yayin rawar daji ta kwanaki 6 masu zuwa, sojojin ruwa na Sin da Rasha za su yi aikin atisaye a fannonin hada kan juna wajen tsaron jiragen ruwa, tsaron sararin sama, fama da hadarin sata, yin aikin ceto, yin aikin jigilar kayayyaki, yin aikin atisayen tafiyar jiragen ruwan soja a karkashin teku da kuma harba wasu harsasai cikin sararin sama. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China