in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta yanke ma wasu yan fashin teku hukuncin rai da rai a gidan yari
2011-10-04 16:53:06 cri
Kamfanin dillancin labaru na kasar sin Xinhua ta ba da labarin cewa wani Alkali a kasar Amurka ranar litinin din nan 3 ga wata ya yanke ma wasu yan asalin kasar Somaliya hukuncin rai da rai a gidan yari saboda laifin fashin jirgin ruwa tare da kashe Amurkawa 2 da matanyen su a teku,inji mai shigar da kara.

Babban Alkalin ya yanke ma Muhidin Salad Omar dan shekaru 30 da haihuwa da Mahdi Jama Mohammed wanda ake kyautata zaton bai wuce shekaru 23 zuwa da 24 ba hukuncin rai da rai a gidan yari ne bisa ga rawar da suka taka a fashin jirgin ruwa da kuma mutuwar wadannan Amurkawa,inji Neil Macbride,babban Alkalin yankin kudancin Virginia.

Omar da Mohammed dukkaninsu yan kungiyar fashin teku ne da suka kwace wani jirgin ruwan kasar Amurka a watan Fabrairu.Masu jirgin ruwan wato Jean da mai gidanta Scott Adam mazauna Marina del Rey,a Jihar Califonia tare da Bob Riggle da mai dakin shi Phyllis Macay mazauna Seattle an harbe su ne bayan da yan fashin jirgin suka rike su garkuwa a nesa da kudancin kasar Oman. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China