Zhang Yesui ya nuna cewa, Koriya tana makwabtaka da kasar Sin, shi ya sa yanayin yankin ke da dangantaka da yanayin karko a kasar Sin. Saboda hakan ne Sin ta mai da hankali sosai kan batun.
A halin yanzu, ya riga ya gana da jakadun kasashe daban daban da abin ya shafa dake kasar Sin don bayyana musu damuwar Sin kan lamarin.
Mr. Zhang ya kara da cewa, kasar Sin ba ta yarda da ko wane bangaren sashen yankin Koriya ba da ya dinga furuci na tsokana, ko gudanar da aikace-aikacen da za su lalata yanayin zaman lafiya da karko a yankin. (Maryam)