Ma'aikatar ta bayyana cewa, a halin yanzu, sojojin kasar kimanin dubu 4 suna gudanar da ayyuka a kasar Mali, daga cikinsu 1200 na arewa maso gabashin kasar Mali. Tun cikin tsakiyar watan Febrairu na bana, sojojin kasar Faransa suka yi musayar wuta sau da dama tare da dakarun reshen kungiyar Al-Qaeda na Islamic Maghreb (AQIM) a yankin arewa maso gabashin kasar Mali. (Zainab)