in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai hari ga wuraren ibada na kasar Nijeriya
2012-06-10 21:49:39 cri
An kai hari ga wuraren ibada na masu bin addinin Krista guda 2 dake Nijeriya a ranar Lahadi 10 ga wata, lamuran da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane, kamar yadda kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin ya ruwaito.

Xinhua ya ruwato majiya na cewar, a birnin Jos na jihar Filato dake arewa maso tsakiyar kasar, an kai harin bom ga wani wurin ibada na St. Agnes Church, inda aka hallaka a kalla mutane 4 tare da raunata wasu 7. Yayin da a birnin Maiduguri na jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar, an yi harbi kan mai uwa da wabi a wani wurin ibada, inda aka kashe a kalla mutane 5, da raunana wasu 15.

Har zuwa yanzu babu rahoto dake bayyana yawan mutanen da suka mutu sakamakon lamuran da gwamnarin kasar ta gabatar, kana ba wata kungiya da ta yi ikirarin daukar alhakinsu.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China