in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi fashewar bom a ofishin 'yan sandan Nijeriya
2011-06-16 22:06:11 cri
Ranar 16 ga wata da safe bisa agogon Nijeriya, an yi fashewar bom a babban ofishin hukumar 'yan sandan birnin Abuja, fadar mulkin kasar, al'amarin da ya haddasa mutuwar wasu mutane, sai dai zuwa yanzu ba a san ainihin adadinsu ba tukuna.

Wadanda suka ganau ba jiyau ba sun ce fashewar bom din ta abku a wurin ajiye motoci na babban ofishin hukumar 'yan sandan birnin Abuja. Tun daga nesa ake ganin hayakin da ya taso daga wajen, har ma ya dade yana ta tasowa.

An ce, mai yiwuwa ne, dakaru masu tsattsauran ra'ayi na kungiyar 'Boko-Haram' ne suka tada bom din, ganin yadda kungiyar ta kai hare-hare da dama a arewacin kasar. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China