Bangaren Sin ya bukaci a yi hakuri da kuma kwantar da hankali kan halin da ake ciki a yankin Koriya
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin ya bayar, an ce, a yayin wani taron manema labaru da aka saba yi a ranar Litinin 11 ga wata, akwai dan jaridar da ya yi tambaya cewa, tun daga yau, kasashen Amurka da Koriya ta kudu sun kaddamar da rawar daji ta shekara-shekara. Sakamakon haka, hukumar Koriya ta arewa ta sanar da cewa, tun daga yau ta yi watsi da "yarjejeniyar kawo karshen yaki a yankin Koriya", har ma ta ce ta daura damarar yaki. Game da wannan halin da ake ciki a yankin Koriya, mene ne ra'ayin gwamnatin kasar Sin?
Game da wannan batu, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, bangaren Sin yana da masaniya game da wannan labarin da aka bayar. Yanzu halin da ake ciki a yankin Koriya yana da sarkakiya sosai. Tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Koriya da yankin arewa maso gabashin Asiya yana dacewa da moriyar dukkan kasashen duniya gaba daya. Sabo da haka, bangaren Sin ya bukaci bangarorin da abin ya shafa da su yi hakuri da kuma kwantar da hankulansu, ta yadda za a iya magance daukar matakan da za su tsananta halin da ake ciki a yankin. (Sanusi Chen)