Gwamnatin kasar Benin na shirin samarwa kasar da wata manufar da ta shafi batun kaura, za ta rika la'akari da 'yan kaka gida, kalubalolin cigaba, kasuwanci, aiki da tsaro, a cewar ministan harkokin wajen kasar Benin, mista Arifari Bako Nassirou a ranar Talata a birnin Cotonou.
"A kasar Benin, baya ga rashin wata manufar kasa ta daidaita batun 'yan kaka gida, sanarwar manufar al'umma (DEPILOPO) ta kasance wata dubara a kasar Benin " in ji mista Arifari tare da bayyana cewa, manufar kaura ta samu cigaba a baya baya dalilin kafa wani tsarin neman cigaba a Afrika na (MIDA), da kungiyar tarayyar Afrika AU ta amince da shi.
"Tsarin MIDA a kasar Benin na ba da kulawa ga 'yan kasar Benin dake zama a kasashen waje dake dogaro kan manyan jigogi biyu da suka hada da shigar da kwarewar 'yan kasar Benin dake waje a fannonin ilmin kimiyya da fasaha da sanya ido kan kudaden da 'yan kasar suke turowa daga kasashe waje."
A lokacin da yake jawabi kan albarkacin ranar kasa da kasa ta 'yan kaka gida domin tunawa da ranar cimma yarjejeniyar kasa da kasa kan kare 'yancin dukkan ma'aikata 'yan kaka gida da iyalensu, mista Arifari ya nuna cewa, kasar Benin na tunawa da wadannan 'yan kaka gida a matsayin masu 'yanci, haka kuma a matsayin wani karfin cigaban kasa. (Maman Ada)