in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Benin ta samu wani tsarin kasa na yaki da cutar Sida a shekaru hudu masu zuwa
2012-12-13 11:04:18 cri

Gwamnatin kasar Benin ta tanadi tsarin aiki na kasa na yaki da cutar Sida da sauran cututtuka na jima'i domin cimma muradun 'babu sabbin masu dauke da wannan cuta, ko mutuwa dalilin wannan cuta da kawar da nuna bambancin dake da nasaba Sida' nan da shekarar 2015, in ji sakatariyar dindindin ta kwamitin kasa na yaki da cutar Sida, forfesa Obey Megnigbeto Antoine a lokacin da take hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Laraba.

Wannan tsarin kasa na yaki da Sida na da burin zama wani makami ga ba da misali kan hanyoyin da za'a bi wajen yaki da wannan annoba a kasar Benin. Kuma hakan zai taimaka wajen karfafa nasarorin da aka samu, matakin da kasa ta dauka kan wannan cuta da kuma aiwatar da matakan dake da nasaba da ba da magungunan kyauta, gwajin jini, bincikin lafiyar mutanen kasar Benin dake fama da wannan cuta, in ji forfesa Obey.

A cewarta, kalubalolin dake gaban kasar Benin su ne raga yawan sabbin masu kamuwa da cutar, yada ta ga sabbin mutane, rage nuna bambanci ga masu fama da wannan annoba, haka kuma da wajabcin hukumomin kasar a wannan batu.

Bisa alkaluman tsarin kasa na yaki da cutar Sida, a shekarar 2012, kasar Benin ta samu sabbin masu dauke da wannan cuta 2600, a shekarar, da mutane 1900 da suka mutu sanadiyyar wannan cuta, lamarin dake nuna cewa, mutane uku ke mutuwa sakamakon cutar a kowace rana. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China