Zababben shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta ya yi alkawari ran Laraba cewa, zai mai da hankalin wajen samar da kyakyawan yanayi da ya dace na kasuwanci da zai kai ga rage tsadar sarrafa kayyayaki da kuma zaman rayuwa.
Da yake jawabi yayin wata ganawa a birnin Nairobi tare da mambobin kungiyar masu harkar kasuwanci na zaman kansu (KEPSA) Kenyatta ya ba da tabbacin cewa, gwamnatinsa ba za ta yi wata tantama ba a yunkurinta na inganta rayuwar jama'ar kasar.
Ya kuma nemi shawarwarin masu harkar kasuwancin kan yadda za'a tsara sabuwar gwamnatin, wacce za ta yi aiki cikin inganci da nufin cika alkawurra da jam'iyyar Jubilee ta yi wa jama'a.
Kenyatta ya ci gaba da cewa, babban buri na gwamnatinsa shi ne hadin kai da kau da bakin ciki tare da jaddada cewa, kasar ba za ta samu bunkasar tattalin arziki ba, sai an samu zaman lafiya da kuma dorewa.
A yayin ganawar, zababben shugaban ya bayyana niyyar gwamnatinsa na yin aiki da sassa masu zaman kansu wajen samar da aikin yi ga matasan kasar.(Lami)