in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin Yang Jiechi ya gana da takwaransa na kasar Zambiya Given Lubinda
2012-05-02 16:40:32 cri
A ranar 2 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Mista Yang Jiechi ya gana da takwaransa na kasar Zambiya Given Lubinda, wanda ke yin ziyara a kasar.

Yang Jiechi ya yi maraba da Lubinda da ya kawo ziyara a karo na farko a kasar Sin, tun bayan da ya hau mukaminsa. Yang Jiechi ya ce, mu'amala ta fannoni daban daban da ke tsakanin kasashen Sin da Zambiya ta kara fadada, kuma hakikanin hadin gwiwa ta kasashen biyu ta kara habaka, kana kuma, bangarorin biyu sun kara yin shawarwari cikin aminci wajen daidaita manyan lamuran duniya. Kazalika kuma, bayan da shugaban kasar Zambiya Michael Chilufya Sata ya hau karagar mulkin kasar, ya jinjinawa irin gudummawar da kasar Sin ta sha bayarwa kasarsa, wajen inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu don raya tattalin arzikin kasarta Zambiya, kuma ya jaddada cewa hakan ya kara karfafa dangantakar bangarorin biyu da ke tsakaninsu, kuma kasar Sin ta yaba da wannan. Haka kuma kasar Sin tana fatan yin kokari tare da kasar Zambiya, don yalwata hadin gwiwa ta sada zumunta da ke tsakanin kasashen biyu ta yadda zai shiga wani sabon mataki.

Bugu da kari kuma, Lubinda ya ce, kasar Sin ta nuna goyon baya ga aikin 'yantar da al'ummomi daban daban na kasar Zambiya, kuma ta ba da fasahohi da dama wajen raya tattalin arzikin kasar Zambiya, kana shugaban kasar Zambiya Sata da gwamnatin Zambiya za su tsaya tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak a duk duniya, kuma za su kara inganta dadaddiyar dangantakar sada zumunta da moriyar hadin gwiwa da ke tsakanin kasashen biyu a karkashin inuwar girmamawa juna da amince da juna.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China