Kasar Sin ta yi kira ga Afirka ta Tsakiya da ta maido da zaman lafiya cikin hanzari
Game da 'yan tawayen Seleka da suka mamaye Bangui, babban birnin kasar Afirka ta Tsakiya a ranar 24 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei ya bayyana a birnin Beijing a ranar Litinin 25 ga wata cewa, kasar Sin tana lura sosai kan halin da ake ciki a kasar Afirka ta Tsakiya, kuma ta damu game da halin siyasa da kasar ke ciki mai tsanani. A cewar Mr Hong Lei, kasar Sin tana kira ga bangarori daban daban na kasar Afirka ta Tsakiya da su yi la'akari da moriyar kasar da jama'arta, su maido da zaman lafiya da kuma tabbatar da shi a kasar cikin hanzari. Kasar Sin tana son yin kokari tare da kasa da kasa wajen taimakawa kasar Afirka ta Tsakiya wajen mayar da zaman lafiya. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku