in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Zambiya ta karyata jita jitar tura matasa zuwa kasar Sudan domin samun horon soja
2012-06-13 13:13:02 cri

Gwamnatan kasar Zambiya ta karyata jita jitar da kafofin kasar ke watsawa na cewa, gwamnatin kasar na shirin aika matasan kasar zuwa Sudan domin samun horon soja, in ji jaridar The Times of Zambia a ranar Talata.

Shugaban babbar jami'iyyar adawa ta biyu mafi girma a wannan kasa, Hakainde Hichilema ya tabbatarwa kafofin watsa labarai na gida cewa ya samu wani labari da dumiduminsa dake cewa gwamnatin kasar na shirin aika matasan jami'yyar hadin kan kishin kasa zuwa kasar Sudan domin samun horon soja.

Mista Hakainde Hichilema ya jaddada cewa, gwamnati ta sanya hannu kan wata jarjejeniya tare da gwamnatin kasar Sudan kan wannan batu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China