in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan Sinawa da suke yawon shakatawa a kasashen waje ya karu da kashi 22.42 bisa 100
2012-01-19 16:46:41 cri

Ranar Laraba 18 ga wata a nan birnin Beijing, shugaban hukumar yawon shakatawa ta kasar Sin Shao Qiwei ya nuna cewa, a cikin shekarar 2011, yawan Sinawa da suka je yawon shakatawa a kasashen waje ya kai kimanin miliyan 70 wanda ya karu da sama da kashi 22 bisa 100.

Shao Qiwei ya yi wannan furuci ne yayin wani taron wakilan hukumomin kula da harkokin yawon shakawata a kasashen waje. Ya ce, Sin na tsayin tsaya daka kan matsayin bude kofa ga kasashen waje tare da yin hadin gwiwa da samun moriya ta gaba daya yayin da ake fuskantar mawuyacin halin tattalin arziki. Kuma ta matakin da ta dauka wajen nuna goyon baya ga jama'ar kasar da su dinga zuwa yawon shakatawa a kasashen waje ba zai canja ba.

An ba da labari cewa, a bara, Sin ta bude kamfanoni uku a wannan fanni wadanda suka jawo jarin kasashen waje, haka kuma, Sin za ta kara mai da hankali a wannan fanni.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China