in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
DRC ta bayyana sake duba takardar ba da lasi ga kamfanonin jiragen sama nan da karshen watan Maris
2013-03-06 14:31:37 cri

Hukumomin kasar DRC-Congo sun bayyana sake duba takardar ba da lasi nan da karshen watan Maris ga dukkan kamfanonin jiragen sama dake kasar, ga kananan jiragen sama da kuma ma'aikatan wannan bangare na sufurin jiragen saman fararen hula, wannan kuma bayan wani hadarin jirgin saman kamfanin CAA da ya faru a ranar 4 ga watan Maris a birnin Goma, in ji ministan sufuri da sadarwa na kasar Justin Kalumba a ranar Talata.

A cewar mistan Kalumba, wani kwamitin bincike da ya hada kwararru na cibiyar binciken haduran jiragen sama, an kafa shi kuma aka tura zuwa wurin da wannan hadari ya abku dake birnin Goma, domin gano musabbabin tarwatsewar wannan jirgi, ta yadda za'a bullo da wasu dokoki, ta yadda za'a rigakafin abkuwar haduran jiragen sama a nan gaba.

Hadarin Goma ya yi sanadiyar mutuwar mutane 6 da mutane uku da suka tsira.

A cewar kuma gwamnan yankin Arewacin Kivu, adadin mutanen da suka mutu ya tashi zuwa 7 yayin da uku suka tsira. A cewarsa, rashin samun ceto cikin lokaci da yanayi su ne dalilan wannan hadari, haka ya bayyana cewa, ana cigaba da neman mutane kuma jami'an kare fararen hula na wurin wannan hadari domin samar da matakan da suka dace. Wani jirgi samfurin Fokker 50 na kamfanin CAA da ya fito daga mahakar ma'adinai ta Lodja dake Kasai-Oriental a tsakiya maso gabashin kasar ya tarwatse a ranar 4 ga watan Maris a birnin Goma. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China