Tawagar sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD a DRC-Congo (MONUSCO), ta kaddamar a kwanakin nan da wani aikin soja mai taken 'Safe Water' a yankin Kudancin Kivu, in ji kanal Felix Basse, kakakin MOMUSCO a yayin wani taron manema labarai da aka shirya ranar Laraba a birnin Kinshasa.
An kaddamar da wannan aiki bisa burin sanya ido kan ayyukan kungiyoyi masu makamai dake kan ruwan kogin Kivu, da kuma kare fararen hula, a cewar mista Basse tare da jaddada cewa, daga ranar 1 zuwa 3 ga watan Maris, dakarun MONUSCO sun gudanar da wani sintiri kan babura da kafa a tsawon cibiyoyin tsaron da aka kafa.
A cewar wannan ofisa na MDD, matsalar tsaro a cikin gundumar Kudancin Kivu, matsala ce dake zuwa lokaci zuwa lokaci, a cikin yanayi zaman dare dare da fargaba dalilin hare-haren dakarun Mai Mai kan sansanonin sojojin DRC-Congo (FADRC) da suka cigaba har zuwa yankunan Walungu, Shabunda da Mwenga.
Kanal Basse ya tunatar cewa, a ranar 1 ga watan Maris, an gudanar da wani babban aikin sintiri a cikin tsarin ayyukan hadin gwiwa masu taken "South sail Board" wato ratsawa ta ruwa har zuwa kudanci da kuma 'Safari Majini' wato ketare ruwa ba tare da tsoro ba tare da jiragen ruwan sintiri na kasar Uruguay da kuma sojojin MONUSCO dake Bukavu. (Maman Ada)