Wan Chen ya ce, sha'anin Intanet na kasar Sin na da makoma mai kyau, kuma zai ba da gudunmawa sosai wajen canja hanyar bunkasa tattalin arzikin kasar ta yadda za ta dace da zamani. Daga baya, gwamnatin kasar za ta ci gaba da kokarin bunkasa Intanet, sa kaimi ga bude kofa ga kasashen waje a wannan fanni, ciyar da ayyukan sarrafa Intanet bisa doka gaba sannan da bunkasa al'adun Intanet yadda ya kamata har ma da tabbatar da tsaron Intanet. Ban da wannan kuma, ya nuna maraba ga kamfanonin Intanet na kasashen ketare da su bude rassansu a kasar Sin.
Kwamishinan kula da harkokin al'adu, sadarwa, sha'anin kirkire-kirkire na kasar Britaniya Mr Ed Vaizey ya bayyana cewa, ana fuskantar zarafi da kalubale baki daya a fannin Intanet, kasashen Sin da Britaniya na da makoma mai kyau wajen yin hadin kai a wannan fanni. Dadin dadawa, Britaniya ta amince da taimakon da Sin ta baiwa nahiyar Afrika wajen bunkasa sha'anin Intanet.(Amina)