A wannan rana, Hu Jintao ya halarci taron shugabannin kungiyar APEC ta fuskar masana'antu da ciniki, inda ya yi jawabin cewa, a halin da ake ciki, dole ne kasashe mambobin kungiyar APEC su yi kokarin kiyaye karuwar tattalin arzikinsu, da tabbatar da ganin ya zauna da gindinsa, ta haka za a iya tallafawa tattalin arzikin yankin Asiya da tekun Pasific, gami da na duniya baki daya.
Har ila yau, Hu ya jaddada cewa, ci gaban da aka samu a kasar Sin shi ne babban dalili ne da ya sa tattalin arzikin yankin Asiya da tekun Pasific da na duniya ke karuwa. Ban da haka kuma, kasar Sin tana maraba da masu kula da masana'antu da cinikayya da ke yankin Asiya da tekun Pasific su yi amfani da damar da bunkasar tattalin arzikin kasar Sin ke samar musu, kana tana son kara hadin kai tare da bangarori daban daban don ciyar da tattalin arzikin yankin Asiya da tekun Pasific, har ma na duk duniya, gaba. (Bello Wang)