Zhang Ping ya nuna cewa, a fannin kara karfin bude kofa, kamata ya yi Sin ta ci gaba da daukar manyan tsare-tsaren samun moriyar juna da kyautata hanyoyin samun bunkasuwa tun da wuri har ma da kyautata tsarin cinikayya tare da kara yin amfani da jarin ketare, sannan da nuna goyon baya ga kamfanonin ketare da su zuba jari a sha'anonin samar da kayayyakin zamani, kimiyyar zamani, ba da hidima, yin tsimin makamashi da sauransu. Dadin dadawa, da kara kyautata tsarin neman zuba jari a kasar Sin, tabbatar da tsarin rigakafin hadarori a ketare domin samarwa kamfanonin kasar Sin wani sharadi mai kyau wajen shiga sauran kasashen duniya.(Amina)