A wajen bikin bude taron dandalin tattalin arziki na Davos na lokacin zafi da ake yi a birnin Tianjin, Mista Wen ya yi jawabin cewa, kasar Sin za ta yi kokarin raya kimiyya da fasaha, gami da kyautata tsarin sana'o'i. Haka kuma za ta yi kwaskwarima kan dokoki da ma'aunin da ake bi, hade da karfafa binciken da ake aiwatarwa kan sana'o'i daban daban. Ban da wannan kuma, kasar za ta yi kokarin tabbatar da daidaituwa tsakanin ci gaban tattalin arziki da na zaman al'umma, inda za ta kara kyautata zaman rayuwar jama'a, da samar da adalci a zamantakewar al'umma. Har ila yau kuma za ta ci gaba da zurfafa gyare-gyaren da ake yi, ta yadda za a tabbatar da samun bunkasuwar tattalin arziki mai dorewa.
Mista Wen ya kara da cewa, kasar Sin tana neman raya kasa tare da bude kofarta, shi ya sa ci gaban da aka samu yana amfanawa bangarori daban daban, don haka kasar za ta ci gaba da tsayawa kan dukkan manufofin da ke goyon bayan manufar bude kofa ga kasashen waje. (Bello Wang)