Kamfanin Fars ya ruwaito wakilin Iran dake hukumar IAEA Ali Asghar Soltanieh yana mai cewa, bangarorin 2 sun kau da wasu daga cikin sabanin ra'ayin dake tsakaninsu, har ma sun cimma matsaya daya kan wasu fannoni masu muhimmanci, kana za su kara kira taron don tattauna shawarwarin da aka gabatar a wannan karo. Sai dai ba'a bayyana fannonin da akacimma ma matsaya a kai ba, balle ma lokaci da wurin da za a kira taron mai zuwa.
Kafin haka dai, hukumar IAEA da Iran sun riga sun yi shawarwari sau da dama don tabbatar da shirin binciken nukiliya. A taron da ya gabata da aka kira a tsakiyar watan Janairun bana, an kasa samun wani ci gaba mai gamsarwa. Hakan yasa hukumar IAEA ta kasa samun damar shiga sansanin Parchin na kasar Iran don gudanar da bincike.
Ban da haka, kasar Iran da sauran kasashe 6 masu ruwa da tsaki a cikin batun nukiliyar kasar, wato su Amurka, Birtaniya, Faransa, Rasha, Sin da Jamus, za su yi taro a Alama-Ata na kasar Khazakstan a ranar 26 ga watan da muke ciki.(Bello Wang)