Don gane da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Mechman Palasite ya bayyana cewa, za a samu sakamako mai gamsarwa cikin shawarwarin da za a yi a makon mai zuwa, muddin dai kasashe shida watau kasashen Amurka, Burtaniya, Faransa, Rasha, Sin da Jamus su amince da ikon kasar Iran kan mallakar nukiliyar.
Yayin taron manema labarai da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta kira a
ranar 19 ga watan nan, Mechman Palasite ya bayyana cewa, kasar Iran za ta kulla yarjejeniya tare da kasashen shida, don kawar da damuwar kasashen duniya, dangane da batun nukiliyar kasar ta Iran, idan suka amince da ikon kasar Iran kan mallakar nulikiya.
Ya kuma kara da cewa, idan kasar Amurka na son yin shawarwari kai tsaye tare da kasar Iran yayin wannan taro, kamata ya yi ta amince da ikon hakan, ta kuma tsayar da takunkumin da ta kakabawa kasar. (Maryam)