in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta fadada takunkumi kan kasar Iran
2013-02-07 11:04:59 cri
A ranar Laraba 6 ga wata gwamnatin kasar Amurka ta kara fadada takunkumi da ta kakaba wa kasar Iran ta hanyar daukar matakan matsin lamba a kan kasar, inda ta kara jerin sunayen cibiyoyi da za ta soke hulda da su.

Sashen baitulmalin Amurka ya ba da bayani cikin wata sanarwa cewa, baya ga bacin tare kudaden shiga daga man fetur na kasar Iran dake waje, sabbin matakan sun kunshi aza takunkumi kan kasar Iran a harkar cinikayya da wasu kasashe, inda hakan zai kara zama da wuya ga kasar Iran ta yi jigilar kudade daga wannan kasa zuwa waccan.

To amma sabbin takunkumin ba su shafi albarkatun gona, kayan abinci, magunguna da kayayyakin lafiya da dai sauransu ba, in ji sanarwar.

An bullo da sabbin takunkumin ne yayin da kasar Iran ta amince ta tattauna da wata kungiya mai suna P5+1 da ta kunshi kasashen Burtaniya, Sin, Faransa, Rasha, Amurka da Jamus ranar 26 ga watan Febrairu a kasar Kazakhstan dangane da batun shirin makaman nukuliya, duk da cewa, kasar Iran ta dage kan cewa, aikin da take yi don amfanin farar hula ne kawai.

Bangarorin 2 sun yi zaman tattaunawa sau uku a shekarar da ta wuce, to amma sun gagara cimma wata matsaya.

Karamin sakatare na yaki da ta'addanci da leken asiri a fannin kudade na baitulmalin Amurka David Cohen ya ce, manufarmu a bayyane take, muddin kasar Iran ta yi biris da damuwar da kasa da kasa ke nunawa dangane da shirin makaman nukiliya, Amurka za ta ci gaba da kakaba mata takunkumi da kuma karin matsin lamba a fannin tattalin arziki. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China