Gidan talabijin din kasar ta Iran ya ruwaito Ali Khamenei na cewa, Amurka ta sha ambaton batun shawarwari kai tsaye tsakaninta da kasar Iran sau da dama, amma ba ta nuna gaskiyar aniyarta ba idan aka yi la'akari da aikece-aikacenta.
Dangane da wannan batu, yayin taron manema labarai da aka saba yi, kakakin majalisar gudanarwa ta kasar Amurka Victoria Nuland ta nuna cewa, ko kasar Iran na son yin shawarwari tsakanin bangarorin shida na kasashen Amurka, Burtaniya, Faransa, Rasha, Sin da kuma Jamus, ko kuma yin shawarwari tsakaninta da Amurka, kasar Amurka za ta amince da duk kudurin da kasar Iran ta tsayar, muddin kudurin zai kawo ci gaba game da warware matsalar nukiliya ta Iran.
Ta kuma bayyana cewa, kasar Amurka za ta ci gaba da matsa lamba ga kasar Iran idan ba ta iya kawar da damuwar da ake nuna wa matsalar nukiliya a kasar ba.
A kuma ranar 7 ga wata, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Ryabkov ya bayyana cewa, kasar Rasha na fatan za a samu sakamako mai gamsarwa a sabon taron shawarwari da ke tsakanin kasar Iran da kasashen shida, kan batun matsalar nukiliya ta kasar Iran da za a yi a birnin Alma-Ata. (Maryam)