• Tsoho Ruz Karacim da iyalansa da suka gaji ladanci daga kakani
Masallacin Itgar yana tsakiyar birnin Kashi dake kudu maso yammacin jihar Xinjiang mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Uygur ta kasar Sin, a ko wace rana da Asuba, wani tsoho mai shekaru kusan 60 a duniya ya isa hasumiyar dake masallacin, don kiran mutanen da suke barci da su farka don zuwa salla. Ruz Karacim shi ne yake ladanci a masallacin.
• Sabon gida na Urayin Semet
Birnin Kashi dake kudu maso yammacin jihar Xinjiang mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Uygur ta kasar Sin, wani tsohon birni ne dake da tarihi na tsawon shekaru 2100 ko fiye. A cikin wannan birnin da yawancin mazaunansa 'yan kabilar Uygur ne, akwai wurare da dama na tsohon yanki da har yanzu suke nuna sigarsu da aka sansu da ita kafin shekaru hudu da suka wuce. Akwai gidaje da yawa da aka gina su da tabo, ga kuma tituna marasa fadi da suke ratsa unguwanni. Yanzu, wadannan tsoffin gidajen da ba su da kayayyakin more rayuwa ba su iya biyan bukatun karuwar mutanen dake zama a wurin.
• Fasahohin koyon Sinanci na iyalan Abullah Mahmud
Malam Abullah Mahmud mai shekaru 69 a duniya, yana zaune ne a wani gari mai suna Bagche na gundumar Hetian ta jihar Xinjiang. Ya yi ritaya daga aikin tukin jirgin kasa. Yayin da yake tuna irin abubuwan da suka abku a lokacin da yake koyon Sinanci, wato harshen kabilar Han ta kasar Sin, ya gayawa wakilinmu cewa, a daidai wannan lokaci, ba a fara yada harshen Sinanci a jihar Xinjiang ba. Wannan ya sa ya koyi Sinanci da kansa.
• 'Yan kabilar Dolan sun nuna kauna sosai ga kide-kiden Muqam
Wakar da kuke saurara yanzu wani babi ne mai taken "Bash Bayawan" da ke cikin kide-kiden gargajiya na Muqam na kabilar Uygur ta jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar Sin, inda aka rera wakar kamar haka:"Ku je ku gai da masoyiyata, ku gaya mata halin da nake ciki. Idan tana so ta fahimci yadda nake ji a rai, to ku gaya mata cewa, ina cikin koshin lafiya kuma na ji dadin zama rayuwata."
• Madam Liu da wasu makwabtanta na 'yan kabilar Uygur
Akwai al'ummomin kabilu daban daban da yawa dake zama tare da juna a jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta kabilar Uygur dake arewa maso yammacin kasar Sin, daga cikin kabilu 47 dake jihar ciki har da kabilun Uygur da Han da Hasak da Mongoliya da sauran kabilu. Akwai banbanci sosai a tsakanin al'ummomin wadannan kabilu daban daban a fannonin zaman rayuwa da al'ada da harsuna da addini, tambayar ita ce yaya suke tabbatar da zaman jituwa a tsakaninsu? Domin amsa wannan tambaya, wakilinmu ya yi tattaki zuwa birnin Yining na yankin Yili mai cin gashin kansa na kabilar Hasak dake arewacin jihar Xinjiang domin ziyartar wani matsugunin kabilar Uygur, wata tsohuwa mai suna Liu Zhixia ta kabilar Han tana zama a wannan wuri.
• Dadin zaman rayuwar Ilham
• Shirin gama kai na samar da harkokin kiwon lafiya a kauyukan jihar Xinjiang
Jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur tana arewa maso yammacin kasar Sin, jihar da kabilu 47 ke zaman rayuwa tare. Daga cikin al'ummar jihar Xinjiang, yawan 'yan kabilar Uygur ya kai kashi 45%, musamman ma an fi samunsu a kudancin jihar, inda akasarinsu suke zaune cikin kauyuka kuma suke ayyukan gona ko kiwon dabbobi. To, amma yaya suke samun harkokin kiwon lafiya kamar yadda manoma da makiyaya a sauran sassan kasar Sin ke samu? Domin amsa wannan tambaya, kwanan baya, wakiliyarmu ta ziyarci Recep Niyazimehmet, wani mazauni wurin.
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China