in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin gama kai na samar da harkokin kiwon lafiya a kauyukan jihar Xinjiang
2010-12-28 10:00:48 cri

Jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur tana arewa maso yammacin kasar Sin, jihar da kabilu 47 ke zaman rayuwa tare. Daga cikin al'ummar jihar Xinjiang, yawan 'yan kabilar Uygur ya kai kashi 45%, musamman ma an fi samunsu a kudancin jihar, inda akasarinsu suke zaune cikin kauyuka kuma suke ayyukan gona ko kiwon dabbobi. To, amma yaya suke samun harkokin kiwon lafiya kamar yadda manoma da makiyaya a sauran sassan kasar Sin ke samu? Domin amsa wannan tambaya, kwanan baya, wakiliyarmu ta ziyarci Recep Niyazimehmet, wani mazauni wurin.

Cikin watan Satumba ne wakiliyarmu ta kai wannan ziyara, kuma a lokacin akwai zafi sosai a gundumar Hetian da ke kudancin jihar Xinjiang. Recep Niyazimehmet, dan kabilar Uygur da ke da shekaru 60 a duniya, ya zauna cikin babban zauren gidansa tare da matarsa, inda jikokinsu biyu suke wasa. Ba don ya fada da bakinsa ba, ba mu yi tsammanin cewa an yi masa tiyata a zuciya ba watanni biyar da suka wuce.

Recep Niyazimehmet ba wani mai kudi ba ne. Shi da matarsa suna dogaro ne ga noman itatuwan tufa da dabino, tare da samun dan kudi kadan kimanin yuan dubu 20 a kowace shekara. Amma tun bayan da ya fara kamuwa da ciwon zuci a shekarar 2004, kudin jinya kawai ya kai kusan yuan dubu 200, musamman ma wajen tiyatar da aka yi masa a zuciya. Amma abin da ya sanyaya masa rai shi ne, yuan dubu biyar ne kawai ya biya wajen wannan babbar tiyatar da aka yi masa. Recep Niyazimehmet ya ce mana,

"Domin wannan tiyata, gaba daya yuan dubu 120 aka biya wannan ya hada da wajen kwana a asibiti da jiyya da kuma abinci, ciki da yuan dubu 90 wajen jiyya, a yayin da gwamnati ta ba da kudin taimako da yawansa ya kai yuan dubu 85."

Recep ya samu wannan taimako daga gwamnati ne sakamakon wani shirin gama kai na samar da harkokin kiwon lafiya da ake gudanarwa a kauyukan kasar Sin. Bisa ga tsarin shirin, manoma da makiyaya suna iya karbar shirin bisa son ransu, kuma mutane masu zaman kansu da gwamnati ne za su zuba kudade ga shirin, domin tallafa wa manoma da makiyaya yayin da suke fama da cututtuka masu tsanani.

An fara gudanar da shirin gama kai na samar da harkokin kiwon lafiya a kauyukan wasu sassan kasar Sin ne tun daga shekarar 2003, kuma bisa ga tsarin shirin, an kara daukar wasu manufofi masu gatanci a jihar Xinjiang, ta yin la'akari da kananan kabilu masu dimbin yawa da ke zaune a jihar da kuma rashin ci gaban tattalin arziki da suke fama da shi. A gundumar Hetian wadda ke fama da talauci, idan manoma da makiyaya suna son amfana da harkokin kiwon lafiya karkashin wannan shiri, yawan kudin da ake bukata daga wajensu hakika ya kai yuan 154.5 a kowace shekara, amma yuan 10 ne kawai za su biya, a yayin da gwamnati za ta biya kudin da ya rage.

Tun bayan da aka fara gudanar da shirin gama kai na samar da harkokin kiwon lafiya a gundumar Hetian a watan Yuni na shekarar 2005, an karbi iyalan Recep cikin shirin, sakamakon dan kudin shiga da bai taka kara ta karya ba da suke samu, har ma sashen kula da harkokin jama'a ya taimaka masa biyan yuan 10 da ake bukata na shiga shirin, hakan nan kuma, Recep ya fara samun kulawa a fannin harkokin kiwon lafiya ba tare da biyan ko sisi ba.

Yayin da ya tuna lokacin da ya kamu da ciwon zuci a shekarar 2004, malam Recep ya ce, a lokacin, ba a fara gudanar da wannan shiri na tabbatar da harkokin kiwon lafiya a wurinsu ba tukuna, sabo da haka, ya kashe kudin ajiyarsa da yawansa ya kai sama da yuan dubu 10 baki daya, har ma ya ari wasu daga wajen 'yan uwansa.

Ruzihan, matar Recep ta ce, a lokacin, likita ya ba su shawarar zuwa asibitin da ya fi kyau, domin a yi wa Recep tiyata a zuciya. Amma babbar tiyata ce, wadda ke bukatar kudi da yawa. A lokacin, ta damu sosai har ta fara tunanin sayar da gidanta. Amma kamar yadda bahaushe kan ce, faduwa ta zo daidai da zama, shirin gama kai na samar da harkokin kiwon lafiya a kauyukan kasar Sin da aka fara gudanarwa a wurinsu ya magance matsalarsu, kamar yadda malama Ruzihan ta ce,

"Ba don shirin gama kai na samar da harkokin kiwon lafiya ba, da ba za mu iya yin wannan tiyata ba, sabo da babu yadda za mu iya tara kudade masu dimbin yawa da ake bukata ba. Mun amfana daga manufofi masu kyau na gwamnati."

Duk da haka, bayan tiyatar, malam Recep na bukatar maganin da zai rika sha a kowace rana, har ma kudin maganin da ya biya a kowane wata ya kai yuan 1800. Yuan dubu 1800 ba kudi kadan ba ne ga Recep da matarsa, amma abin da ya faranta musu rai shi ne, shirin da suka karba ya taimaka masa biyan rabin kudin maganin. Malam Recep ya yi murna da cewa, yanzu makwabtansa da 'yan uwansa ma sun karbi shirin. Mirnisa Tursuntohti, likitar da ta taba yi wa malam Recep jiyya a gundumar Hetian, ta ce mana,

"A da, wadanda suka kamu da cutar sankara, ba damar su samu jiyya, sabo da sun kasa biyan kudin jiyya, al'amarin da zai iya kai su ga mutuwa. Amma yayin da suka karbi shirin, yanzu suna ta zuwa asibitinmu, su ma wadanda suka kamu da cututtuka marasa tsanani, ko mura ne ko kuma ciwon kai, suna ta zuwa wurinmu, domin suna amfana daga wannan shiri na gama kai na samar da harkokin kiwon lafiya."

Yanzu haka a gundumar Hetian, manoma da makiyaya suna iya karbar wannan shiri a duk lokacin da suke bukata. Rabia Abdulrahman, shugabar sashen kula da harkokin kiwon lafiya a gundumar Hetian ta bayyana mana cewa, ya zuwa yanzu, yawan manoma da makiyaya da suka karbi shirin ya kai kashi 99.2% na mutanen gundumar Hetian, wato kowa na da tabbaci ke nan. Sa'an nan, bisa labarin da hukumar kula da harkokin kiwon lafiya ta jihar Xinjiang ta bayar a shekarar 2010, an ce, an fara gudanar da shirin a gundumomi daban daban na jihar, wanda har ya hada da manoma da makiyaya sama da miliyan 10. Sai mu ce, shirin yana ba da kariya ga lafiyar manoma da makiyaya a jihar ta Xinjiang. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China