in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsoho Ruz Karacim da iyalansa da suka gaji ladanci daga kakani
2010-12-28 10:16:36 cri

Masallacin Itgar yana tsakiyar birnin Kashi dake kudu maso yammacin jihar Xinjiang mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Uygur ta kasar Sin, a ko wace rana da Asuba, wani tsoho mai shekaru kusan 60 a duniya ya isa hasumiyar dake masallacin, don kiran mutanen da suke barci da su farka don zuwa salla. Ruz Karacim shi ne yake ladanci a masallacin.

Akwai musulmai kimanin miliyan 2.5 dake zaune a birnin Kashi na jihar Xinjiang, kuma akwai masallatai da yawansu ya kai 803 a wurin. Masallacin Itgar da tsoho Ruz Karacim ke ladanci shi ne masallacin da ya fi girma a jihar Xinjiang, har ma a duk kasar Sin, kuma yana daya daga cikin masallatai guda goma da suka fi girma a yankin tsakiyar Asiya. Tsoho Ruz yana ladanci a masallacin na tsawon shekaru 25 da suka wuce. A shekaru fiye da goma da suka wuce, Ruz a lokacin da shekarunsa na haihuwa suka kai 7 ne ya soma koyon karatun Alkur'ani, daga baya kuma ya koyi ladanci daga wajen babansa, bayan da babansa ya mutu, ya soma ladanci a masallacin Itgar.

'Mahaifina ya yi ladanci a masallacin Itgar na tsawon shekaru 60. Kuma na gaje shi bayan mutuwarsa. Ladanci a masallaci, don kira musulmai zuwa ga salla a masallaci, a Musulunci wannan aiki ne mai daraja a gare mu. Saboda haka, na yi farin ciki da gada mahaifina.'

Yin salla sau biyar a ko wace rana, wani muhimmin sashi ne na zaman rayuwar yau da kullun na musulmai. A ko wace rana, akwai musulmai fiye da dubu daya dake zuwa masallacin Itgar don yin salla. A ranar karamar salla, da babbar salla, yawan mutanen da suka zo masallacin za su kai dubu 70 zuwa 80. Tsoho Ruz yana yin alfahari da samun damar ba da hidima ga musulmai, a sa'i daya kuma ya samu girmamawa daga musulmai da kuma gwamnatin jihar. A ko wane wata, hukumar kula da harkokin addinai ta wurin tana ba shi kudin Sin RMB yuan 1500, don nuna goyon baya ga aikinsa.

Yin aikin hajji a Mekka, wani babban nauyi ne dake kan musulmai. Tun bayan da aka aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen ketare, gwamnatin kasar Sin ta dawo da aikin tura kungiyoyin da za su rika yin jagoranci ga masu zuwa aikin hajji, saboda haka, yawan musulman kasar Sin da suka je birnin Makka mai tsarki don yin aikin hajji yana ta karuwa. A birnin Kashi kuma, bayan da aka bude zirga-zirgar jiragen sama tsakanin kasa da kasa kai tsaye, musulman birnin suna iya tashi daga garinsu zuwa Mekka kai tsaye, ba tare da yada zango a birnin Urumqi, hedkwatar jihar Xinjiang, ko birnin Beijing ba. Saboda haka, akwai musulmai sama da 1000 da suka je Mekka daga birnin Kashi a ko wace shekara. Tsoho Ruz shi ma ya je aikin hajji a shekarar 2005.

A hakika dai, baya ga harkokin addini, akwai wasu abubuwa na zaman rayuwar yau da kullum da tsoho Ruz ke gudanarwa. Iyalansu sun koyi kasuwanci daga kakakinsu, haka kuma sun samu dukiyoyi da dama. A shekaru goma da suka wuce, tsoho Ruz ya kashe kudin Sin RMB dubu 350 don gyara gidansa mai hawa biyu, wannan kudi ya yi yawa a wancan lokacin. Yanzu, iyalinsa su 11 suna zama tare cikin farin ciki, yaransu kuma sun girma.

'Dana na farko yana aiki a kungiyar wake-wake da raye-raye ta jiharmu, dana na biyu yana kasuwanci a wani wuri dake kusa da masallacin Itgar, dana na uku kuma yana koyon karatun Alkur'ani daga wajen limanin masallacin Itgar, yana shirin zama wani mahaddacin Alkur'ani, dana ta karshe kuma yana aiki a ofishin sayar da tikitin jiragen sama.'

Saboda ya tsufa, don haka, ya ke neman wani magaji mai dacewa, don ci gaba da yin ladanci a masallaci, wannan ya zama matsalar da tsoho Ruz ya kan yi la'akari da ita. Yanzu, kusan za a ce ya samu amsar tunanin da yake yi, wato 'dansa na uku, Mirahmetcan zai gaje shi.

Mirahmetcan yana kula da wani kanti tare da 'dan uwansa a kusa da masallacin Itgar, inda suke sayar da kayayyakin ado, da abubuwan sha. Saboda bunkasuwar sha'anin yawon shakatawa, yawan kudin shiga da suke samu yana karuwa. Amma, duk da haka, nufinsa shi ne zama wani ladani a masallaci.  

'Kakana ya yi ladanci a masallaci, yanzu mahaifina shi ma yana ladanci, kamata ya yi na gaje shi, saboda iyalanmu, da kuma wannan aiki mai tsarki.'

Domin ya gaji mahaifinsa yadda ya kamata, bayan da ya gama karatu a makarantar sakandare, a ko wane mako Mirahmetcan ya kan je masallacin Itgar, don koyon karatun Alkur'ani daga wajen limaman masallacin, bayan da ya koma gida kuma, ya kan ci gaba da karatu. Saboda kokarin da ya yi na tsawon shekaru takwas da suka wuce, yanzu haka yanahaddace Izu 30 na Alkur'ani.

Mirahmetcan da shekarunsa na haihuwa suka kai 22 yana da shirin yin aure ba da dadewa ba. Ya gaya mana cewa, yariniyar da zai yi aure ita ma ta zo ne daga birnin Kashi, kuma ta gama karatu a wata jami'a ba da jimawa ba. Za su shirya wani bikin aure na gargajiyar kabilar Uygur, inda za su gayyaci babban Limamin masallacin Itgar don ya shugabanci bikinsu. Mirahmetcan na nuna kyakkyawan fata ga zaman rayuwarsu nan gaba. Ya ce, yana fatan za su haifi yara guda uku, kuma yana fatan daya daga cikinsu zai gaje shi, don ci gaba da zama ladani, da ba da hidima ga musulmai na wurin.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China