in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon gida na Urayin Semet
2010-12-28 10:14:49 cri

Birnin Kashi dake kudu maso yammacin jihar Xinjiang mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Uygur ta kasar Sin, wani tsohon birni ne dake da tarihi na tsawon shekaru 2100 ko fiye. A cikin wannan birnin da yawancin mazaunansa 'yan kabilar Uygur ne, akwai wurare da dama na tsohon yanki da har yanzu suke nuna sigarsu da aka sansu da ita kafin shekaru hudu da suka wuce. Akwai gidaje da yawa da aka gina su da tabo, ga kuma tituna marasa fadi da suke ratsa unguwanni. Yanzu, wadannan tsoffin gidajen da ba su da kayayyakin more rayuwa ba su iya biyan bukatun karuwar mutanen dake zama a wurin.

Urayin Semet mai shekaru 60 a duniya yana zama tare da iyalinsa a tsohon birnin Kashi. An gina wannan tsohon gida da suke zama a ciki da katako, da tabo, wanda ke kunshe da dakuna sama da 10 da suka gada daga kakaninsu, irin wannan gidan da ba shi da na'urori na zamani ba sa iya samar da muhalli mai kyau ta fuskar kiwon lafiya, har ma suna iya kawo illa ga rayuwar mutanen dake zama a ciki. Urayin ya gaya mana cewa, 'An gina tsohon gidanmu da tabo da katako, ko da yake akwai dakuna da yawa, amma ba su da girma.'

Birnin Kashi yana yankin da aka fi samun girgizar kasa. Bisa nazarin da gwamnatin birnin Kashi ta yi an gano cewa, yawancin gidajen dake tsohon yankin birnin ba su iya jure bala'in girgizar kasa ba. Saboda haka, a watan Yuni na shekarar 2009 gwamnatin birnin ta soma aiwatar da wani ayyukan yin gyare-gyare na gwaji kan tsohon yankin. Iyalin Urayin Semet ya zama daya daga cikin iyalan da suka ci gajiyar wannan aiki. Bayan da aka soma yin gyare-gyare a gidansa, Urayin ya kan je wurin don ganin yadda ake aiwatar da wannan aiki a gidansa a ko wace rana, kuma ya yi farin ciki sosai. Urayin ya gaya mana cewa, 'A karkashin taimakon da gwamnatinmu ta bayar, an gyara gidanmu ta hanyar amfani da rodi tare da kankare (reinforced concrete). Amma, ba a canja sigarsa ba. Dakunan dake sabon gida sun fi girma bisa na da, kuma an fi iya ganin wayewar safiya.'

An gina sabon gidan Urayin a wurin da tsohon gidansa yake, wanda ke da dakuna guda 17, fadinsa ya kai muraba'in mita 250. Gwamnatin birnin Kashi ce ta bayar da kudin gyare-gyaren ginshikin gidan, kana shi kuma ya biya kudin sayen kofofi da tagogi, da kuma yi wa gidan ado. Adadin kudin da aka kashe a sabon gida ya wuce RMB dubu 300, amma ya biya yuan dubu 120 ne kawai.

A karshen shekarar 2009, Urayin ya kaura zuwa sabon gidansa tare da iyalinsa. Sabon gida ya fi girma akan na da, sannan an kara wasu na'urori a ciki kamar tarho, da na'urar kama shirye-shiryen talibijin, da intanet, kana an gina sabon bayan gida. Bayan haka kuma, ana iya dafa abinci da wanka ta hanyar yin amfani da ruwan fanfo, da gas.

Iyalin Urayin sun nuna gamsuwa sosai kan sabon gidansu. Tilakiz, 'yarsa ta karshe da shekarunta na haihuwa suka kai 12, ta jagorancinmu shiga dakinta, ta kuma gaya mana cewa, 'Ina son ajiye wani gado a nan, da kuma wani kantar litattafai a can. Bayan haka kuma, ina bukatar na'urar kamputa. Zan mai da hankali ga karatuna, ina son in zama lauya a karshe.'

Iyalin Urayin suna alfahari sosai da sabon gidansu, 'yaanuwansu da abokansu su kan kawo musu ziyara, wasu kuma su kan zauna na 'dan gajeren lokaci. Urayin ya gaya mana cewa, 'Yanayin gidanmu ya samu kyautatuwa, wasu 'yan uwanmu dake karkara su kan kwana a gidanmu a yayin da suka zo birnin. Wani dangina da shekarunsa na haihuwa suka wuce 70 yana zama a gidanmu, yana iya zuwa ko tafiya a duk lokacin da yake so. Muna lale marhabin da zuwansu a ko wane lokaci.'

A shekaru fiye da goma da suka wuce, iyalin Urayin na samun kudin shiga ne ta hanyar saukar da mutanen dake karkara yayin da suka zo sayen kayayyaki, ko neman aikin yi a birnin. A da, saboda ba su da wuraren kwana masu kyau, shi ya sa bakin da suka kwana a gidansu su kan biya kudin RMB yuan 1 kawai a ko wace rana. Amma, bayan da suka gina sabon gida, yanayin wuraren kwana sun samu kyautatuwa sosai, wannan ya sa iyalin Urayin za su samu kudin shiga yadda ya kamata. Urayin ya ce, 'Na bayar da hayar dakuna guda biyar, amma bayan lokacin sanyi kuma, za mu kara wasu gadaje da na'urori a cikin sauran dakunan, bayan da aka shiga yanayin bazara zan sake bude karamin hotel din, a lokacin za a biya a kalla yuan 5 a ko wace rana.'

A shekarar 2009, akwai iyalai sama da 8600 da suka taba zama a tsohon yankin birnin Kashi kamar yadda iyalin Urayin suka sun kaura zuwa sabbin gidaje. Bisa shirin da gwamnatin birnin Kashi ta yi, a cikin shekaru hudu masu zuwa, iyalan da yawansu zai kai dubu 65 za su samu sabbin gidajensu.

Ayyukan yin gyare-gyare kan tsohon yanki na birnin Kashi ya samu yabo sosai daga bangarori daban daban. Jami'an kungiyar UNESCO ta MDD sun yi bayani bayan da suka yi bincike kan sabbin gidajen cewa, bayan da aka yi gyare-gyare kan tsohon yankin, duk da haka an kiyaye siga ta musamman na tsoffafin gidaje, da kuma al'adar zaman rayuwa ta gargajiya ta mazauna wurin, wannan ya nuna manufar mayar da babbar moriyar jama'a a gaban kome, wanda kuma na dacewa da misalin kasashen duniya, kuma fasaha ce da ta cancanci a yada ita.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China