in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fasahohin koyon Sinanci na iyalan Abullah Mahmud
2010-12-28 10:13:25 cri

"Wannan shi ne abinci mai suna Sanzi, 'yan kabilar Uyghur mu kan ci irin wannan abinci. Ana toya shi cikin mai. Kuma babu gishiri da yawa a ciki. Sai ku dandana. Bismilla!"

Da zarar malam Abullah Mahmud ya ga cewa, mu baki ne daga wuri mai nisa sosai, ya kan bayyana mana yadda hada irin wannan abinci da Sinanci, tare da ba mu abincin gargajiyar kabilar Uyghur.

Malam Abullah Mahmud mai shekaru 69 a duniya, yana zaune ne a wani gari mai suna Bagche na gundumar Hetian ta jihar Xinjiang. Ya yi ritaya daga aikin tukin jirgin kasa. Yayin da yake tuna irin abubuwan da suka abku a lokacin da yake koyon Sinanci, wato harshen kabilar Han ta kasar Sin, ya gayawa wakilinmu cewa, a daidai wannan lokaci, ba a fara yada harshen Sinanci a jihar Xinjiang ba. Wannan ya sa ya koyi Sinanci da kansa. Malam Abullah Mahmud ya bayyana cewa, "A lokacin, babu wani darasi game da koyon harshen Sinanci a jihar Xinjiang. Mun tilasta wa kanmu wajen koyon Sinanci. Kafin wannan kuma, Ina aikin tukin jirgin kasa a hukumar jiragen kasa. A daidai wancan lokaci, wanda yake koya mini da fasahohin tukin jirgin kasa, dan kabilar Han ne daga yankin arewa maso gabashin kasar Sin. Wannan shi ne dalilin da ya sa na koyi Sinanci domin saukin fahimtar juna."

A matsayinsa na matukin jirgin kasa, koyon Sinanci ba ma kawai ya taimaka sosai ga malam Abullah Mahmud a fannin aikinsa ba, har ma ya ba shi zarafi da yawa wajen kai ziyara a wurare daban daban na kasar SIn. A cikin wadannan shekarun da suka gabata, Abullah Mahmud ya taba kai ziyara a biranen Beijing, da Shanghai, da Guangzhou, da Hongkong, da kuma Macau, inda ya bude idonsa sosai. Ta haka ya kasance daya daga cikin mazauna garin Bagche da suka fi ziyartar wurare da samun ilmi.

Sabo da ya fahimci muhimmancin koyon harshen Sinanci, shi ya sa malam Abullah Mahmud ya bukaci dukkan 'ya'yansa biyar da su samu tarbiyyar Sinanci, har ma daya daga cikinsu ya kasance malamin koyon Sinanci a wata makarantar midil a halin yanzu. Wannan tsoho ya bayyana mana cewa, "Koyon Sinanci zai ba da taimako a fannonin aiki da zaman rayuwa duka a nan gaba. Shi ya sa yana da muhimmanci sosai. Idan ba a koyi harshen Sinanci ba, to ba za a samu ci gaba yadda ya kamata ba."

Ba kamar yadda malam Abullah Mahmud ya koyi harshen Sinanci a'a tilas ba, dansa na farko mai suna Ablet ya nemi ya koyi Sinanci bisa radin kansa. Bayan da ya kammala aikinsa a rundunar soja, Ablet ya fara aiki a ofishin 'yan sanda dake garinsu, inda ya gamu da matsaloli da dama a sakamakon rashin iya Sinanci. A sabili da haka, ya shiga wani darasin koyon Sinanci a jami'ar Xinjiang da kansa. A daidai wannan lokaci, albashin da Ablet yake samuwa kadan ne. Ba shi da karfin biyan kudin karatu duka. Amma ba wata-wata, mahaifinsa Abullah Mahmud ya taimaka masa a wannan fanni, inda ya ba shi kudi har zuwa lokacin da ya kammala karatunsa a jami'ar.

Ya zuwa yanzu, shi ma Ablet ya samu haihuwa, wato yana da da daya da diya daya. Diyarsa tana yin karatu a wata makarantar midil, yayin da dansa yake karatu a cibiyar makarantar firamare ta garin Bagche. Ablet ya bayyana fatansa cewa, 'ya'yansa za su kara samun karatu yadda ya kamata. Ba ma kawai za su koyi harshen Sinanci ba, hatta ma za su koyi wani harshen kasashen waje. Kuma za su kai ziyara a wurare daban daban na kasashen duniya domin bude idanunsu a nan gaba. Ablet ya furta cewa, "'Ya'yana suna karatu. Duk irin matsalolin da za su gamu da su, zan taimaka musu. Muddin ba za mu yi kokarin warware irin wadannan matsaloli ba, to za mu ari kudi a wajen sauran mutane. Sabo da dole ne 'ya'yana su je makarantu su samu ilmi. Yanzu an samu bunkasuwa sosai a babban yankin kasar Sin, haka ma a duniya baki daya. Idan har za su samu zarafin ziyartar wasu kasashen waje, to zan ba su goyon baya tare da ba da taimakon kudi."

Dan Ablet mai suna Alimcan yana aji na uku a cibiyar makarantar firamare ta garin Bagche a halin yanzu. Ko da yake karami ne, amma yana da ra'ayoyin kansa. Ya bayyana mana cewa, mahaifinsa ya zama jarumi a cikin zuciyarsa. Shi ya sa dole ne ya koyi harshen Sinanci yaddaya kamata, a kokarin kasancewa wani dan sanda kamar yadda mahaifinsa yake yi a yanzu, domin ba da kariya ga al'umma da kasar Sin baki daya.

A kokarin biyan bukatun 'yan kananan kabilun kasar Sin na samun kyakkyawar tarbiyya da ilmin kimiyya da fasaha na zamani, jihar Xinjiang ta Uyghur mai cin gashin kanta tana zuba jari tare da samar da ma'aikata da yawa, a kokarin ba da tarbiyya ta hanyar amfani da harsuna biyu, wato harshen Sinanci da yaren kananan kabilu a cikin dukkan makarantun firamare da na midil a wannan yanki. Kawo yanzu dai, an fara ba da tarbiyya ga kananan yara kafin shiga makarantun firamare a garin Bagche ta harsuna biyu, wato harshen Sinanci da yaren kabilar Uyghur. Yayin da wakilinmu ya yi tambayar cewa, ko ana damuwa cewa yara za su manta da harshe da al'adun kabilarsu a sakamakon samun tarbiyya bisa harsuna biyu, malam Ablet ya kada kai, inda ya gayawa wakilinmu cewa, "Ba mu nuna damuwa ko kadan ba. Sabo da yara su ma suna samun wasu darussa game da 'yan kabilar Uyghur. Alal misali, yara suna samun darasin harshe bisa yaren kabilar Uyghur, yayin da suke samun sauran darussa bisa harshen Sinanci a makaranta. Dadin dadawa, bayan da yara suka koma gida da dare, mu kan yi magana da harshen kabilar Uyghur a harkokinmu na rayuwa."

Bayan haka kuma, Ablet ya fahimcicewa, koyon Sinanci ba ma kawai zai taimaka a fannonin aiki da rayuwa ba, har ma zai taimaka a sauran fannoni. Ya bayyana cewa, "Kasar Sin tana kunshe da kabilu iri daba daban. Idan mu 'yan kananan kabilu ba mu iya harshen Sinanci ba, to wannan zai kawo babbar illa wajen samun bunkasuwa tare. A sabili da haka, idan muna neman samun ci gaba tare da juna, dole ne mu koyi harshen Sinanci cikin yakini. Bayan haka kuma, koyon Sinanci zai ba da gudummawa wajen hada kan kabilu daban daban na kasar Sin. Hakan yana da kyau kwarai da gaske."

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China