in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Madam Liu da wasu makwabtanta na 'yan kabilar Uygur
2010-12-28 10:03:33 cri

Akwai al'ummomin kabilu daban daban da yawa dake zama tare da juna a jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta kabilar Uygur dake arewa maso yammacin kasar Sin, daga cikin kabilu 47 dake jihar ciki har da kabilun Uygur da Han da Hasak da Mongoliya da sauran kabilu. Akwai banbanci sosai a tsakanin al'ummomin wadannan kabilu daban daban a fannonin zaman rayuwa da al'ada da harsuna da addini, tambayar ita ce yaya suke tabbatar da zaman jituwa a tsakaninsu? Domin amsa wannan tambaya, wakilinmu ya yi tattaki zuwa birnin Yining na yankin Yili mai cin gashin kansa na kabilar Hasak dake arewacin jihar Xinjiang domin ziyartar wani matsugunin kabilar Uygur, wata tsohuwa mai suna Liu Zhixia ta kabilar Han tana zama a wannan wuri.

Gidan Liu Zhixia yana titin Xinhua mai lamba 22 na unguwar Topcu dake birnin Yining. A yayin da wakilinmu ya shiga gidanta, ya ga dakuna 7 da wasu gonakin da aka shuka kokwamba da gauta da kuma barkono a ciki, ban da haka kuma, an sanya wasu kejin kaza a wurin dake dab da gonakin.

A yayin da madam Liu ta ga wakilinmu, ta yi masa maraba, sannan ta ba shi kankana da inabi da kuma sauran abincin kananan kabilu. Daga bisani, ta fara hira tare da wakilinmu.

"An haifi ni a yankin Yili, kuma na girma a nan, kakanin-kakanina sun kaura zuwa nan daga lardin Hebei a lokacin daular Qing. Ina shekaru fiye da 50 da haihuwa, na yi ritaya daga aiki, a da, na yi aiki a wani kamfanin dake karkashin jagorancin hukumar tattalin arziki da ciniki."

Madam Liu ta gabatar da cewa, mijinta ya gaji wannan gida daga kakaninsa, mijinta da ita sun yi aure a nan kafin shekaru 30 da suka gabata. Amma akwai nisa sosai a tsakanin wannan gidan da wurin aikinta, shi ya sa, ta kan zauna a birni, kuma ta komo gida a karshen kowane mako. Bayan da ta yi ritaya daga aikin da take yi kafin shekaru 3 da suka gabata, ita da mijinta sun kaura zuwa nan daga birni domin jin dadin zaman rayuwa. A yayin da wakilinmu ya tambaye ta game da bambancin dake tsakanin wannan wuri da birni, madam Liu ta bayyana cewa, "A birni, kowa yana cikin gida, ya rufe kofar gidansa. A sakamakon ayyukan da mutane suka yi, ba su da damar yin wata hira ko tattaunawa. Amma a nan, makwabta su kan zo gidana mu yi hira. Idan suna son cin abincina, su kan dauka ko da ba tare da samun amincewa ba, a ganina, akwai 'yanci sosai a wannan wuri, wannan bambanci ne dake tsakanin mutanen wannan wuri da birni."

Gidan madam Liu yana karkarar birnin Yining ne, inda akwai iyalai kimanin 30 ko fiye, ciki har da iyalai 7 ko 8 na kabilar Han, sauran iyalai su ne 'yan kabilar Uygur ne. A game da makwabtanta na kabilar Uygur, madam Liu ta ce, "A wannan wuri, babu bambancin dake tsakanin kabilar Uygur da kabilar Han, muna iya harshensu, su ma suna koyon harshen Sinanci. Mun sada dankon zumunci a tsakaninmu. Alal misali, makwabta su kan ba ni abinci da suka dafa, kana ni ma na kan ba su abinci masu dadin ci. A lokacin bikin yanayin bazara, su kan kawo ziyara a gidana, muna zama tamkar 'yanuwa."

Akwai wani karin magana na kasar Sin, wato dangogin dake da nisa bai fi makwabta ba. Madam Liu ta ce, kamar yadda wannan karin magana ya bayyana, 'yan kabilar Han da 'yan kabilar Uygur suna zama tare cikin jituwa, duk wanda ya gamu da wata matsala, to makwabtansa za su ba shi taimako, ta ce, "Wata macen dake makwabtaka da mu ba ta da miji, kuma tana da wani yaro, wata rana, yaronta ya yi tuntube, sai kafarsa ta ji rauni, sabo da haka, muka tara kudi, kowane makwabci ya ba ta taimako gwargwadon karfinsa domin ta yi jinyar yaronta."

Madam Liu ta ce, a hakika dai, makwabta sun sada dankon zumunci ta hanyar ba da taimako ga juna.

Al'umomin kabilu daban daban sun zama tare, a sakamakon banbancin al'ada da ra'ayoyi, mutane su kan samu sabani a wani lokaci. Madam Liu ta ce, idan aka samu sabani a tsakaninsu, su kan tattauna domin daidaita wannan matsala cikin jituwa. Ta kara da cewa, "Kananan kabilu suna da al'adunsu na musamman, idan aka fahimci al'adunsu, wannan zai kara sa a zauna tare da su cikin jituwa, kuma za a sada zumunci tare da su. Ban da haka, ya kamata, al'ummomin kananan kabilu su fahimci al'adun sauran mutane."

Kabilu daban daban dake zama a jihar Xinjiang sun dade suna zama da kuma aiki tare, sun yi koyi da juna, shi ya sa, suka kafa zaman al'umma na musamman na jihar Xinjiang. Madam Liu ta ce, "Lalle muna da tasiri ga juna, yanzu, mu kan sha ti tare da nono da safe, mun riga mun saba da haka, ban da haka kuma, mu kan ci abincin kananan kabilu, a lokacin bikin bazara, mu kan taya murnar bikin bazara ta hanyar tsarin kananan kabilu da kabilar Han, kana mun samu tasirin da mutanen kananan kabilu suka kawo mana wajen karbar baki. A bangaren daban, a lokacin da, mutanen kananan kabilu ba su da kayan lambu, amma yanzu, domin irin tasirin da muka yi musu, sun fara cin kayan lambu kamar yadda muke yi."

A yayin da muke hira da madam Liu, makwabtanta sun gayyace mu zuwa gidansu….

Ko da yake a gidan makwabcinta, madam Liu ta maraba da mu tamkar uwar gida, a game da haka, mai gida Mollahon bai ji mamaki ba, ya ce, "A jihar Xinjiang, al'ummomin kananan kabilu ba su iya rabuwa da al'ummomin kabilar Han ba, kana mutanen kabilar Han ba su iya rabuwa da al'ummomin kananan kabilu ba, muna kasancewa kamar a iyali guda." (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China