in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dadin zaman rayuwar Ilham
2010-12-28 10:01:52 cri

Yau, mun shiga cikin wani gida na kabilar Uyghur da ke da hawaye 2, fadinsa ya kai murabba'in mita 240, an yi kawata mai kyau a ciki wannan daki, kuma an cika kayayyaki da dama da ke nuna al'adu na kabilar Uyghur, haka kuma, akwai wani babban talabijin da ya dauki hankalin jama'a sosai. A cikin wannan gida, nan ba da dadewa ba, 'ya 'yan itatuwa za su nuna, haka kuma, mai gida yana zaune ne a karkashin inuwa.


Sunan mai gida shi ne Ilham Yakup, dan kabilar Uyghur da ke siriri sosai kuma yana da kunya. Uwargidansa Nurgul tana da kyaun gani, kuma tana son baki sosai, haka kuma yayin da aka tabo maganar gidanta, Nurgul ta yi alfahari da cewa,"Wannan shi ne gidanmu na 4, a wancan gari, muna da gidaje 2, a wannan gari, mun gina gidaje 2. A lokacin zafi, mu kan zama a nan, a lokacin sanyi, mu kan zama a can babban gini. Haka kuma ko da yake, muka yi ciniki har na shekara guda ne kawai, amma albashinmu ya kai kudin Sin Yuan dubu 70, haka kuma muna da yankunan kasa, sabo da akwai mutane da suka haya yankunan kasarmu, watau gaba daya albashinmu ya kai samar da dubu 100 a ko wace shekara."


Dalilin da ya sa Nurgul ta yi alfahari da gidanta, sabo da a kauyen Daxi da ke gundumar Weili ta yankin Bayingeleng, Ilham ya isa samu kudi sosai.
A shekarar 1991, Ilham Yakup ya ci jarrabawar shiga cikin kwalejin koyon ilmin tattalin arziki na jihar Xinjiang, ya zama dalibi na farko a kauyen Daxi. Sabo da mahaifiyarsa ba ta cikin koshin lafiya, a sakamakon haka, a matsayinsa na babban yaro a gida, bayan da ya kammala karatu a kwalejin, ya koma garinsa, kuma ya yi sana'ar aikin gona, kuma yana kulawa da iyalinsa. Yayin da ya samu lokacin hutu, ya kan koyon Sinanci, don dinga samun ilmi da karuwa.


A lokacin shekaru 90 na karnin da ya wuce, bayan da zaman rayuwar jama'ar jihar Xinjiang, ya samu ingantuwa sosai, Ilham ya gano cewa, yayin da matasa suke yin aure, su kan nemi masu daukar hoton Bidiyo, sabo da haka, ya sayi wani Bidiyo, kuma ya koyi fasahohi daukar hoton bidiyo, kuma ya fara sana'arsa ta daukar hoton bidiyo ga bikin aure. Ya waiwayi baya da cewa,"A wancan lokaci, ba a samu mai daukar hoton bidiyo a gundumar Weili ba, bayan da zaman rayuwar jama'ar jihar Xinjiang ya samu kyautatuwa, kuma jama'a su kan shirya gagarumin bikin aure, sabo da haka, ina zato cewa, idan na nemi wani da ya zo in taimake ni don daukar hoton bidiyo, zai kashe kudi da dama. Haka kuma, yayin da nake karatu, na koyi wasu fasahohi, sabo da haka, na sayi wani bidiyo, kuma kasuwa ta ci, ta waste."


Sabo da haka, a lokacin farko, Ilham ya samu wadata daga sha'anin daukar hoton bidiyo ga sauran jama'a, haka kuma bayan da ya gano cewa, gwamnatin Sin ta sa kaimi ga manoma da su kara shuka auduga, ya yi amfani da kudin ajiya don kara shukar auduga, kuma fadin yankunan auduga da ya shuka ya karu daga ekka 15 zuwa ekka fiye da 200. Haka kuma, bayan da ya duba, tattalin arziki ya samu bunkasuwa sosai, aka bukatar sufurin kayayyaki da yawa, ya sayi motoci, don yin sana'ar sufurin kayayyaki na dogon zango, haka kuma, bayan da ya tarar cewa, aka kara samun mutane da dama da suke son kaura zuwa manyan gine-gine, kuma akwai matsalar wanke darduma, ya yi sana'ar wanke darduma. Haka kuma, ya zuwa yanzu, sabo da sana'ar abinci ta bunkasa sosai, ya bude wata masana'antar tsabtace kayayyakin cin abinci a gundumar.


Yayin da ya waiwayi tarihin aikinsa, Ilham ya ce, dalilin da ya sa, ya iya gano damar yin ciniki, sabo da ya samu ilmi da iyawa yayin da yake karatu a jami'a. Ya ce,"Bayan da na kammala karatu a jami'a, na iya koyon ilmi cikin sauki, kuma ina zato cewa, wannan shi ne abin da na koya a jami'a."


Yayin da na yi hira da mai gida, dansa Elizat ya dawo gida, kuma ya je sayen abinci ga kare a gidansa. Elizat mai shekaru 11 da haihuwa, wani dalibi ne a firamare na gundumar Weili ta jihar Xinjiang, ba ma kawai ya iya yaren Uyghur ba, haka kuma ya iya harshen Sinanci sosai, idan aka kwatanta shi da sauran abokan yara, Elizat shi ma yana son Cartoons, kuma yana son wasa da abokansa. Ya ce,"Ina son wasan kwallon kwando da kwallon kafa da wasannin Badminton."


Ilham ya gaya mana cewa, ya yi shawarwari da uwargidansa, ba za su ci gaba da haihuwa ba, kuma za su yi kokari don kyautata zaman rayuwarsu, da samar da kyakkyawan sharadi a fannin ilmi ga yaronsu. Ya ce,"Ina zato, yaro guda ya ishe ni, sabo da ina son, dana zai iya kokarin karatu, bayan da ya girma, zai shiga jami'a mai kyau, har ma, idan akwai yanayi, zai je dalibta a kasashen waje, zan yi kokari don samun kudi, shi ma zai yi kokarin karatu."


Zaman wadata ya kawo sauyin tunani ga haihuwar yara a jihar Xinjiang, Ilham ya gaya mana cewa, abokan gari suna son zaman tare sosai. Yanzu, an kafa kwamitin 'yan gari a kauyen Daxi, shi ma yana daya daga cikin membobi na kwamitin 'yan gari na wannan kauye, kuma ya samu ikon yin sharhi game da batutuwan da ke aukuwa a kauyen. Ilham ya ce, ya riga ya kafa kamfanin yin hidima a kauyen Daxi, kuma yana fata zai iya  kara yin ciniki, don 'yan garin Daxi za su iya zaman wadata tare. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China